✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kai wa sansanin sojoji hari a Katsina

’Yan bindiga sun kai wa sansanin sojoji hari a Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Gungun ’yan bindiga sun kai wa wani sansanin sojoji hari a kauyen Nahuta a Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Ganau sun ce yadda da misalin karfe 11 na daren Lahadi ne ’yan bindigar suka yi wa sansanin sojojin da ke wurin kawanya.

Daya daga cikin sojojin da abin ya shafa, wanda aka sakaya sunansa, ya ce, harin ya zo masu kwatsam daga kuma bangarorin daban-daban.

Ya ce maharan sun kona motocinsu biyu, amma babu wanda ya rasa ransa a harin.

Rahoton ya bayyana cewa wasu daga cikin sojojin ba su dawo daga hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara ba a lokacin da aka kawo harin.

Al’ummar yankin sun kara da cewa maharan sun tafi da dabbobi bayan sun shiga cikin garin inda suka rika buxe shaguna suka kwashi kayan abinci.

Har dai zuwa rubuta wannan rahoto babu wani bayani da ya fito daga ’yan sanda bayan tuntubarsu da wakilinmu ya yi.