✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kai harin farko a garin Batsari

Sun kashe mutum daya, wasu 27 sun yi batar dabo.

’Yan bindiga sun afka wa garin Batsari da ke Jihar Katsina a karon farko, inda suka kashe mutum guda suka kuma yi awon gaba da wasu da dama.

Wani mazaunin garin, ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa wani manomi, Iliya Bakon-Zabo, shi ne mutumin da aka kashe a harin.

“Dazu, wata mata ta dawo, don haka ba za mu iya cewa ko duk wadanda suka bace suna hannunsu a yanzu ba ko a’a, amma a halin yanzu mun kirga mutum 27 da ba mu san inda suke ba,” inji shi.

Ya ce ’yan bindigar sun shiga garin Batsarin ne da misalin karfe 12.10 na talatainin daren Laraba suka fara harbi babu kakkautawa.

Karon farko ke nan da ’yan bindigar suka shiga garin Batsari sakamakon duk hare-haren da suka gabata a Karamar Hukumar an kai su ne a kauyuka.

Sai dai ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar tarwatsa ’yan bindigar, wanda ba don kokarin da jami’an tsarno, da munin lamarin ya fi haka.

Kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce ’yan sanda da sojoji sun yi nasara fatattakar ’yan bindigar.