✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun harbi mutum biyu tare da yi wa mata fyade a Sakkwato

An kai harin ne Karamar Hukumar Sabon Birni da ke Jihar Sakkwato.

’Yan bindiga sun harbi mutum biyu a kauyen Adamawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato.

Shugaban Kungiyar ’yan sa-kai a yankin, Musa Muhammad da aka fi sani da Bulaki ya sanar da haka, inda ya ce harin ya faru ne a daren Lahadi, sannan ’yan binidgar sunje kauyen Rambadawa, inda suka yi wa wadansu magidanta duka tare da yin fyade ga wadansu mata.

An samu labarin sun yi fashi a Dantasakko da Nasarawa da Gidan Idi har sun tafi da baburan mutanen kauyen.

A yankin akwai gungun mahara da ke da shugabanni daban-daban wadansu daga cikinsu su ne Nagona da Jambo Baki da Usaini Dankwano da Dan Bakolo da Bello Turji da sauransu.

Hare-hare a yankin ya yi sauki sosai, wanda ya sa mutanen Karamar Hukumar Isa ke bin hanyar Gundumi da gwamnati ta rufe tsawon lokaci kan matsalar tsaro duk da ba a samu sanarwar bude hanyar a hukumance ba.