✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbi alkali da ɗansa, sun sace mutane 13 a Katsina

Maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga cikin ’ya’ansa.

’Yan bindiga sun kai hari garin Mahuta da ke Ƙaramar Hukumar Kafur a Jihar Katsina, inda suka harbi wani alkali, Rabiu Mahuta, a hannu da kuma dansa.

A lokacin harin na daren Talata, maharan sun raunata mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 13, ciki har da matar alƙalin da kuma biyar daga cikin ’ya’ansa.

Wani mazaunin garin da ya zanta ya ce ’yan bindigar sun isa wurin ne da misalin karfe 11:30 na dare, kuma kai tsaye suka nufi gidan alkalin, inda suka kwashe kusan awa guda suna ƙoƙarin karya ƙofar gidan.

Duk da kiran da alƙalin ya yi wa DPO na yankin domin neman taimako, jami’an tsaro ba su iso a kan lokaci ba.

Ya ce, “Da suka samu nasarar shiga gidan, nan take sun harbe shi a hannu, sai ya faɗi a ƙasa. An kuma raunata ɗansa da raunin harbi a goshinsa.”

Wani makwabcinsa, wanda kuma mamba ne a hukumar tsaron al’umma ta jihar da ya yi ƙoƙarin kai ɗauki a lokacin harin, shi ma an harbe shi kuma yana karɓar magani a wani asibiti a Katsina a halin yanzu.

Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutane biyar a gidan wani mai suna Shehu Maishayi, tare da Malam Sufi Nahi da kuma matar Malam Abdurrazak, wanda ke zaune a wajen garin Mahuta.

Majiyoyi sun ce sojoji sun iso ne kawai bayan da ’yan bindigar suka tsere daga wurin.