Akalla mutum 19 ne ’yan bindiga suka harbe har lahira bayan sun kai hari wata kasuwar da ke garin Unguwar Lalle a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato ranar Juma’a.
Harin ya kuma yi sanadiyyar jikkata mutane da dama, wadanda akasarinsu yanzu aka kai Babban Asibitin Sabon Birni inda suke samun kulawa.
- Amurka ta fara hawa teburin tattaunawa da ’yan Taliban
- ‘Yadda muka yi kwana 53 muna cin ciyawa a hannun masu garkuwa da mu’
Sai dai Aminiya ba ta iya tantance ko harin na ramuwar gayya ba ne ko kuma a’a, sakamakon zaman dar-dar da ake yi a yankin tun bayan da wasu mambobin haramtacciyar kungiyar ’yan sa-kai suka hallaka mutum 11 a kasuwar kauyen Mamande ranar Alhamis.
Unguwan Lalle, wanda kauye ne da ke kan hanyar Goronyo zuwa Sabon Birni ya sha fama da hare-haren ’yan bindiga a ’yan watannin nan, inda har sojoji biyar aka taba kashewa.
Wani mazaunin yankin ya tabbatar wa da Aminiya cewa an kai hari ne a kan kasuwar wacce take ci sati-sati lokacin da ake tsaka da hada-hada.
Kasuwar dai na daya daag cikin manyan kasuwanni a Gabashin Jihar Sakkwato da take hada mutane daga Jihohin Kebbi da Zamfara da ma Jamhuriyar Nijar.
To sai dai ba a iya tantance mutanen da aka kashe ba, ko da dai wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa daga cikin wadanda aka harbe din har da wasu ’yan gida biyu da ke sana’ar sayar da fata.
“Biyu daga cikinsu daga cikin garin Sakkwato suka shigo. Yanzun nan ma muka kammala jana’izarsu a makabartar Tudun Wada da ke Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu,” inji majiyar.
Rahotanni dai sun ce ’yan bindigar sun yi wa kasuwar kawanya ne jim kadan da dawowar mutane daga sallar Juma’a, inda suka rika harbin kan mai uwa da wabi.
“Na kirga gawarwaki ni kaina guda 19, sannan akwai wadanda har yanzu ba a san inda suke ba,” ini majiyar.
Laifin ’yan kasuwa ne – Gwamnati
To sai dai gwamnatin Jihar ta zargi ’yan kasuwar da cewa su suka jawo harin saboda ta hana cin dukkan kasuwannin da ke Gabashin Jihar don dakile ayyukan na ’yan bindiga.
Kwamishinan Al’amuran Tsaro na Jihar, Kanal Garba Moyi (mai ritaya) ne ya bayyana hakan yayin tattaunawarsa da wakilinmu.
“Gwamnatin Jiha ta hana cin kasuwanni a wasu sassa na Jihar nan saboda matsalar tsaro bayan mun gano a nan ’yan ta’adda suke sayen kayayyakin amfaninsu.