Akalla mutum 10 ne wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne suka harbe ranar Litinin suna kan hanyar zuwa cin kasuwa a kasar Burkina Faso.
Wani jami’in gwamnati a yankin ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AIB cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutum hudu yayin harin.
- Ya kamata Majalisar Tarayya ta hana bara a kan tituna —Ganduje
- Hukumar NEDC za ta gina makaranta a Yobe
An kai harin ne kan mutane da ke cin kasuwa a kauyukan Dambam Markoye da ke dab da iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar.
Garuruwan dai na da nisan kimanin kilomita 16 daga kan iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar.
Kazalika, AIB ya rawaito cewa tuni sojojin kasar su ma suka mayar da martanin gaggawa a yankin don kaucewa kai wani sabon harin.
Galibi dai mazauna garin na Dambam kan tafi Markoye don cin kasuwa duk ranar Litinin ko dai a kafa, ko a babur mai kafa uku ko kuma a keken shanu don cinikin dabbobi.
Kasar Burkina Faso dai kamar makwabtanta da dama a yankin ma fama da matsalolin tsaro na ayyukan ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma ’yan bindiga.