’Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da garkuwa da wasu shi a garin Erena da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja a daren Asabar.
Mayiyarmu ta ce ’yan bindiga dauke da muggan makamai ne suka yi dirar mikiya a garin na Erena —karon farko da ’yan ta’adda suka kai hari garin.
- An rufe makarantar da ’yan bindiga suka kwashi dalibai a Kaduna
- Shekara 5 bayan rabuwarsu, ta dawo gidan tsohon mijinta ta casa amaryarsa
- Dalibai 39 ne ba a gani ba bayan harin Kaduna
- Yadda muka dakile yunkurin sace dalibai a makarantar ’yan Turkiyya a Kaduna —Sojoji
“Sun afka wa jama’ar garin ne yadda suka ga dama, abin takaici kuma ba tare da fuskantar turjiya ba ko fatattaka daga mahukunta.
“Karin abin takaici shi ne an bar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, kuma wadanda ba sa dauke da makami su yi ta kansu,” inji majiyar.
Ta cewa yanzu matsalar ’yan ta’adda masu garkuwar da mutane don karbar kudin fansa kafin sakin su ya zama ruwan dare a yankin.
A cewarta, hare-haren ’yan bindiga sun gurgunta harkokin tattalin arziki tare da jefa al’ummar yankin cikin halin kaka-nika-yi.