Aƙalla mutum 10 ne suka rasu, yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon harin da wasu mahara suka kai wa al’ummar Ruwi da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos, a Jihar Filato.
Maharan sun kai harin ne a daren ranar Alhamis, inda suka buɗe wuta kan mutanen da suka halarci wata jana’iza da misalin ƙarfe 9:30 na dare.
Wani mazaunin yankin ya ce: “Mummunan hari ne. Sun zo kwatsam suka fara harbi. Muna roƙon hukumomin tsaro da su ɗauki mataki don kare al’ummarmu.”
Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar harin, amma ba ta bayyana adadin waɗanda suka rasu ba.
Kakakin rundunar, DSP Alabo Alfred, ya ce, “Kwamishinan ‘yan sanda ya tura ƙarin jami’an tsaro da kayan aiki don wanzar da zaman lafiya.
“Za mu tabbatar da cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun fuskanci hukunci.”
Gwamnatin Jihar Filato ta yi Allah-wadai da harin.
Kwamishiniyar Yaɗa Labarai ta jihar, Joyce Ramnap, ta tabbatar wa jama’a cewa ana ɗaukar matakan kawo ƙarshen irin waɗannan hare-hare.
“Gwamnati ba za ta lamunci kashe rayukan ‘yan ƙasa ba. An umarci hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci.”