Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin.
- Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang
- NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu
Wani mazaunin Isa, Basharu Altine Giyawa, ya ce, “Tun a ranar Asabar muka samu bayanai cewa Turji zai ziyarci Gatawa, kuma mun sanar da hukumomi.
“Duk da haka, shi da mutanensa sun bi ta ƙauyukanmu, sun yi bikin sallah, sannan suka kashe manoma 11 a hanyarsu ta komawa Fakai.”
Ɗan majalisar dokokin Jihar Sakkwato mai wakiltar yankin, Hon. Aminu Boza, ya tabbatar da samun rahoton harin.
Amma ya ce: “Turji bai ziyarci kowace unguwa a yankina domin yin sallah ba. Mun ɗauki matakin gaggawa bayan samun bayanai, wanda hakan ka iya zama dalilin da ya sa ya mayar da martani kan waɗannan manoman a Isa.”
Mazauna yankin sun bayyana damuwa kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da ƙaruwa, duk da ƙoƙarin jami’an tsaro.
Sun yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen magance matsalar domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Hukumomin tsaro har yanzu ba su fitar da wata sanarwa kan harin ba, amma majiyoyi sun bayyana cewa sojoji na bin sahun Turji domin daƙile ayyukansa a yankin.