✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

 ’Yan bindiga sun harbe masu yawon Sallah, sun sace wasu mutum 2 a Katsina

Lamarin ya faru ne a hanyar dawowa daga Jibiya

Wasu ’yan bindiga sun harbe wani dalibi, sun kuma sace wasu mutum a kan hanyarsu ta komawa Jibiya daga Katsina bayan sun je yawon Sallah.

Lamarin ya faru ne a Kwarare da ke kan hanyar zuwa Jibiya a ranar Litinin da misalin karfe 9:00 na dare a cewar wani abokin marigayin da suke tafiya tare a lokacin da abin ya faru.

Abokin mai suna Muhammad Aliyu wanda ya kuma tsallake rijiya da baya, ya shaida wa Aminiya yadda abin ya faru, inda ya ce suna dawowa ne daga bikin Sallah a Katsina.

Sannan ya ce, sun yi arangama da ‘yan bindigan ne yayin da suka tare kan titin da suke tafiya da wasu manyan itatuwa, lamarin da ya talista wa wasu motoci uku, ciki har da wacce suke ciki su tsaya.

Sai dai a cewarsa, motar farko da ke gabansu direban ya yi cikin daji a kokarinsa na kauce wa itacen, kuma Allah ya taimake shi ya tsere.

Amma ya ce ta ritsa da su da kuma motar da ke bayansu.

Ya ce, “Nan take ‘yan ta’addan suka harbi direban motarmu a kafa, da suka yi kokarin sace marigayin da sauran mutane biyun sai ya yi kokarin ya gudu, su kuma suka harbe shi”.

“Sai su ka yi awon gaba da wasu mutane biyu daga daya motar da kuma mutum daya daga ta mu,” inji Muhammad.

Dalibin da aka harbe mai suna Anas Adamu dai na shekarar karshe ne ta karatu a Kwalejin  Gwamnatin Tarayya da ke Katsina.

Aminiya ta tuntubi Kakakin ta ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, wanda ya ce ba shi da labarin afkuwar lamarin, amma zai tuntubi Baturen ‘Yan Sanda na Jibiya.