’Yan bindiga sun harbe wani ma’aikacin filin jirgin saman Kaduna da ke aiki da Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya (NAMA), mai suna Shehu Na’Allah.
Na’Allah ya gamu da ajalinsa ne lokacin da maharan suka yi yunkurin shiga filin jirgin ranar Asabar, bayan sun yi musayar wuta da jami’an tsaroa a kusa da filin, kodayake ba su samu damar shiga ba.
- An yi musayar wuta da ’yan bindiga a kusa da filin jirgin saman Kaduna
- Gwamnan Bauchi ya ba zakarun musabaka ta kasa kyautar miliyan uku-uku
Lamarin dai ya tilasta soke tashin wani jirgi da ke shirin zuwa Legas daga filin.
Wata majiya ya tabbatar wa Aminiya cewa, “Daya daga cikin ma’aikatan filin da ke aiki da hukumar NAMA ya gamu da ajalinsa a hannun ’yan bindigar, amma babu abin da ya samu jirgin.
Wata majiya a cikin filin ta ce babu jirgin da aka kai wata hari.
A cewar majiyar, tilas kasancewar ’yan bindigar kusa da filin jirgin ta sa aka dakatar da tashinsa.
Daga bisani dai an ce an girke jami’an sojoji a filin don dawo da doka da oda.
Duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.