✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe Janar din soja

Kwanan nan aka nada shi a matsayin Darakta a Hedikwatar Sojin Kasa.

Wasu ’yan bindiga sun harbe Manjo-Janar Hassan Ahmed, wanda kuma Darakta ne a Hedikwatar Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun kashe Janar Ahmed ne a daren ranar Alhamis a yankin Abaji da ke Birnin Tarayya, Abuja sannan suka yi garkuwa da matarsa.

  1. Masu juna biyu sun mutu wajen rububin karbar abinci a Borno
  2. ’Yan bindiga sun kashe sojoji biyu a Sakkwato

Janar Ahmed shi ne tsohon Shugaban Sashen ’Yan Sanda na  Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya.

Wata majiya ta bayyana cewar Janar din sojan da matarsa na kan hanyarsu ta zuwa garin Okene ne Jihar Kogi ne a lokacin da ’yan bindigar suka kai musu farmaki.

“Sun bude wa motarsa wuta, nan take ya mutu. Amma direbansa ya yi karyar mutuwa ko da suka karasa wajen sai suka yi awon gaba da matarsa,” a cewar majiyar.

A baya-bayan nan, Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Farouk Yahaya, ya nada Janar Ahmed a matsayin Darakta a Hedikwatar Rundunar Sojin Kasar da ke Abuja.