✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun harbe jami’an hukumar shige da fice 2 a Katsina

An yi rashin sa’a jami’ai biyu sun kwanta dama.

Wasu ’yan bindiga da ake zargi ’yan daban daji ne sun harbe jami’ai biyu na Hukumar Shige da Fice ta Kasa a Jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne da duku-dukun ranar Alhamis yayin da ’yan bindigar suka kai hari Kauyen Kadobe da ke Karamar Hukumar Jibia.

Wata majiya mai tushe ta ce jami’an sun rasa rayukansu yayin musayar wuta da ’yan bindigar suka kai hari kauyen.

A cewarta, “ba a taba kai wa kauyen hari ba kasancewar akwai sansanin Hukumar Shige da Fice da ke yankin saboda haka akwai aminci da har ta kai makiyaya da dama sun dawo nan tare da dabbobinsu.

“Akwai lokuta da dama da ’yan bindiga suka yi yunkurin kawo hari ba tare da samun nasara ba, sai dai a wannan karo kaddara ta riga fata.

“Sun kawo wannan sabon harin da misalin karfe 12.05 na dare, inda a kokarin jami’an Hukumar Shige da Ficen na dakile harin suka fara musayar wuta da ’yan bindigar.

“Sai dai a karshe an yi rashin sa’a jami’ai biyu sun kwanta dama,” a cewar majiyar.

Rahotanni sun ce da dama daga cikin ’yan bindigar sun rasa rayukansu yayin da wasunsu suka tsere da rauni na harsashin bindiga, a sakamakon musayar wutar.

Sai dai Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindigar sun samu nasarar tserewa da gawawwakin wadanda aka kashe daga cikinsu tare da wasu shanu da suka sata na makiyaya a kauyen.

“Sojojin da ke sintiri a yankin sun yi gaggawar kawo agaji inda suka shiga aka rika musayar wutar da su, wanda a dalilin haka aka harbi soja daya a cinyarsa.

Majiyar ta kara da cewa, “A halin yanzu sojan da aka harba yana samun kulawa a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Katsina.”

Wani jami’in tsaro da ya bukaci a sakaya sunansa, y ace daya daga cikin jami’an da aka kashe, Umar Bagadaza Kankara, tuni aka yi jana’izarsa bisa koyarwar addinin Islama a cibiyarsa ta garin Kankara.

Ya ce, dayan kuma mai suna Lauwali Dutse, an garzaya da gawarsa mahaifarsa da ke garin Dutse a Jihar Jigawa domin sanya shi a makwancin karshe.

Yayin da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Hukumar Shige da Fice na Jihar Katsina, Iliyasu Kasimu, ya ce ba shi da hurumin cewa komai a kan lamarin har sai ya samu izini.