✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun harbe gandirobobi 2 a Anambra

Wasu a bindiga a jihar Anambra sun hallaka jami'an Hukumar Kula da Fursunoni biyu, yayin da suke kan hanyarsu ta kai fursunoni kotu a ranar…

Wasu ‘yan bindiga a jihar Anambra sun hallaka jami’an Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali wato Gandirobobi biyu, yayin da suke kan hanyarsu ta kai fursunoni kotu a ranar Juma’a.

Kamfanin Dillacin Labarai (NAN) ya rawaito cewar lamarin ya faru da misalin karfe 11 na safiyar Juma’a, a yankin Ekwulobia, a Karamar Hukumar Aguata.

Harin na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan sojin ruwa, inda suka bude musu wuta tare da yin awon gaba da makamansu.

Bayan harin ‘yan bindigar sun bar fursunonin daure cikin motar da aka dauke su zuwa kotu.

Sai dai wani shaidar gani da ido, ya bayyana cewa wasu daga cikin jami’an da fursunonin sun tsere yayin harin, yayin da biyu daga ciki kuma suka rasa rayukansu.

Kakakin Rundunar ‘Yan SandanJjihar, DSP Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar harin.

Sai dai ya ce rundunar na ci gaba da fadada bincike don gano wadanda suka aikata laifin.