Wasu ’yan bindiga sun kashe daliget uku na zaben Gwamnan jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja.
Shugaban kwamitin zaben kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo, ne ya sanar da haka a sakatariyar jam’iyyar PDP ta Jihar, inda aka gudanar da zaben fid da gwani a Minna.
- 2023: PDP ta tsayar da ’yan takarar Gwamna 2 a Kano
- Zaben fid da gwanin PDP: Daliget 2 ne suka zabi Shehu Sani a Kaduna
An ce an kashe wakilan ne a ranar Laraba, yayin da suke komawa Mariga bayan da jam’iyyar ta dage zaben fid da gwanin sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan takarar suka yi ta nuna rashin amincewa da jerin sunayen wakilan.
Daga nan ne aka bukaci wakilan da su kawo katin shaida don tantance sunayensu kafin gudanar da zaben da aka canja zuwa ranar Alhamis.
Tuni dai aka cike gurbin wadanda suka rasa rayukansu don cike gibin adadin wakilan Karamar Hukumar.
Daya daga cikin wakilan, Shehu Haruna, ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne a tsakanin Mariga da Tegina kuma mutane hudu ne suka rasu.
A cewarsa “Mun bar Minna ne sa’o’i kadan bayan PDP ta dage zaben fid da gwani na Gwamna zuwa ranar Alhamis, kuma mun koma don kawo katin zabe da sauran shaidar tantancewa.
“Muna kan hanyar komawa gida ne muka yi kacibus da ’yan bindiga, wanda nan take suka bude wa motarmu wuta. Ko da ya ke mun tsere tun da ba su harbi direban ba, amma mutum hudu nan take suka mutu,” inji shi.
Ya ce Karamar Hukumar da ke kan iyaka da Birnin-Gwari a Jihar Kaduna ta zama maboyar ’yan bindiga da ke kai hare-hare ba kakkautawa.
Haruna ya yi kira da a samar da jami’an tsaro na dindindin a yankin da za su kare matafiya da al’ummomin yankin.