‘Yan bindiga sun kashe wani shaihin malami a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya ( ABU), Dokta MB Hassan a lokacin da yake bakin aikinsa a Zamfara.
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni Barista Solomon Dalung ya sanar da mutuwar marigayin a shafinsa na sada zumunta inda ya bayyana kisan shaihin malamin da abun bakin ciki
” Kaico! Mun yi babban rashi.
“Yanzu nake samun labarin cewa ‘yan bindiga a Zamfara sun kashe Dokta MB Hassan na tsangayar binciken al’amuran noma na Jami’ar ABU a lokacin da yake bakin aiki.
“Allah Ya rahamshe shi, Allah ya kawo mana karshen wannan bala’i.
“Wannan babban rashi ne, kuma da yawa sun rasa ransu a hannun ‘yan bindiga, Allah ya sanya Aljannah ce makomarsa” kamar yadda Solomon Dalung ya rubuta a shafinsa na facebook.
Kafin rasuwar Dokta MB Hassan jami’i ne a Tsangayar Binciken Al’amuran Noma na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.