✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun hallaka sama da mutum 50 a Katsina 

Maharan sun dinha harbi kan mai uwa da wabi a ƙauyen.

Aƙalla mutum 50 ne suka rasa rayukansu, yayin da kuma aka sace wasu da dama ciki har da mata da ƙananan yara, sakamakon ƙazamin harin da ’yan bindiga suka kai ƙauyen ’Yargoje da ke ƙaramar hukumar Ƙankara a Jihar Katsina.

Wasu majiyoyi daga ƙauyen, sun bayyana cewar wasu tarin ’yan bindiga a kan babura sun afka wa ƙauyen da yammacin ranar Lahadi, inda suka jikkata mutane da dama, tare da yin awon gaba da wasu da dama.

Wani mazaunin ƙauyen, Hassan Ya’u, ya shaida wa manema labarai cewar, ’yan ta’addan sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi, inda suka kashe mutum sama da 50.

Kazalika, ya ce a harin ya yi sanadin mutuwar ɗan uwansa.

Wani mazaunin garin, Abdullahi Yunusa Kankara, ya ce ya tsallake rijiya da baya sakamakon harin.

Ya ce ƙauyen nasu ya zama dandalin kisa, saboda babu wani gida da ba a kashe mutum a cikinsa ba sakamakon wannan harin.

Amma ya ce a yanzu haka suna aikin tantance yawan mutanen da suka mutu da waɗanda suka jikkata.

Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin Arewa Maso Yamma da ke ci gaba da fuskantar hare-haren ’yan bindiga a Najeriya.