’Yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutum bakwai a cikin sa’o’i 72 a Kananan Hukumomin Chikun da Kajuru da Giwa da ke Jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa ranar Asabar, ya ce jami’an tsaro ne suka tabbatar wa da Gwamnatin Jihar hare-haren.
- NDLEA ta kama mutum 7, ta lalata kadada 22 ta gonar Tabar Wiwi a Edo
- ’Yar aiki ta tsere da jaririn gidan da take aikatau a Kaduna
A cewarsa, ’yan bindiga sun harbe mutum hudu a kusa da garin Tsohon Gayan da ke Karamar Hukumar Chikun.
Aruwan ya kuma ce wasu ’yan bindigar sun kashe mutum biyu da aka bayyana sunansu da Solomon Bamaiyi da Francis Moses a kauyen Kakau na Karamar Hukumar ta Chikun, sai kuma wani da ba a tantance sunansa ba a Karamar Hukumar Kachia.
Kwamishinan ya kuma ce an kashe wani mai suna Danjuma Alhaji, dan asalin garin Tsohon Farakwai da ke Karamar Hukumar Igabi, a garin Galadima na Karamar Hukumar Giwa.
Samuel Aruwan ya ce Gwamna Nasiru El-rufa’i ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan tare da addu’ar neman gafara garesu.
Ya kara da cewa jami’an tsaro sun kai ziyarar karfafa gwiwa zuwa yankin tashar Iri inda aka kashe wasu mazauna garin tare da yin garkuwa da wasu da dama.