✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun hallaka mutum 17 da tsakar rana a kauyukan Zamfara

Mazauna yankin sun ce maharan sun farmaki kauyukan nasu ne ranar Alhamis

’Yan bindiga sun hallaka akalla mutum 17 a kauyuka hudu da ke Karamar Hukumar Anka ta Jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce maharan sun farmaki kauyukan ne ranar Alhamis, inda suka rika harbi ta ko ina.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun yi wa kauyen Kadaddaba dirar mikiya da tsakar rana, ba tare yin wani abin da zai jawo musu farmakin ba.

Wani mazaunin yankin mai suna Malam Hussaini ya ce, “Sun zo a kan babura, lokacin da muke fitowa daga masallaci bayan idar da sallar Azahar.

“Mun ankarar da mutanen da ke kusa da mu, sannan muka gudu cikin dazuka. Amma sai suka rika bin mutanen daga ke kokarin guduwa suna harbe duk wanda suka gani.

“Sun kashe mutum 10 a kauyenmu, ciki har da sirikina.

“A kauyen Rafin Doka kuwa, sun harbe mutum daya, biyu kuma a Babban Baye, hudu kuma a kauyen Wano. Dukka kauyukan a kurkusa da juna suke.

“Maganar da nake da kai yanzu haka, ina garin Anka inda na samu mafaka,” inji shi.

Ya kuma ce tun da farko maharan sun kai farmaki kasuwar garin Rafin Gero, inda suka yi awon gaba da dabbobin da aka kawo don sayarwa.

“Sun kuma kwashi kayayyaki da dama daga shagunan mutane, wadanda suka farfasa. Akwai ma rahotannin da ke cewa sun kashe mutane a can, amma ba zan iya fada maka adadinsu ba yanzu,” inji shi.

Duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.