Wasu ’yan bindiga sun hallaka mutum 13 a kauyen Taro dake Karamar Hukumar Sabon Birni ta jihar Sakkwato.
Aminiya ta kuma gano cewa karin wasu mutum bakwai kuma sun samu munanan raunuka kuma yanzu haka suna can suna samin kulawa a asibiti sakamakon harin.
- ‘Yadda yunkurin yi wa wata fyade ya sa yanzu na daina haihuwa’
- Har yanzu ina nan a kan baka ta kan shawarar yi wa ’yan bindida afuwa – Sheik Gumi
A cewar Dagacin kauyen na Tara, Mainasara Muhammad Tara, maharan sun kuma yi awon gaba da dabbobi da dama tare da kone rumbunan adana hatsi na garin.
“Sun zo da misalin karfe 11:58 na rana ta wata hanyar da ba a cika bi ba wajen shiga garin saboda matasanmu na gadin kusan dukkan manyan hanyoyin shigowa garin.
“Ba ma iya ko rintsawa ba sakamakon yawan harin da ake kai mana ba kakkautawa.
“Sun silalo ne ta wata barauniyar hanya dake Gabas da gari sannan suka budewa mutum biyu da muka ajiye ta wannan yankin wuta tare da kashe su nan take.
“Daga nan ne kuma suka shiga cikin garin tare da kashe duk wanda suka ci karo da shi.
“Yanzu haka ba mu jima da binne mutane 13 ba, ciki har da wata yarinya mai shekaru shida da wasu mutum bakwai da muka garzaya da su asibiti inda suke samun kulawa,” inji Dagacin.
Sai dai ya yi korafin cewa jami’an rundunar tsaron hadin gwiwa da suka ankarar tun da farko a kan harin ba su yi wani katabus wajen kawo musu dauki ba.
Ya kuma ce wannan shine karo na biyu a cikin watanni biyu da ake kawowa kauyen nasu hari, inda ya ce yayin harin na baya sama da dabbobi 200 ne aka yi awon gaba da su.
Da aka tambaye shi ko za su ci gaba da zama a kauyen duk da harin sai ya ce, “Ba mu da inda za mu je da ya fi nan kwanciyar hankali. Ba zai yuwu mu kyale kauyenmu ba saboda wannan harin, mun riga mun rasa komai daga dabbobi zuwa abinci.”
Da wakilinmu yua tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar ta Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar ya yi alkawarin bayar da bayani idan ya dawo daga kauyen.
“Yanzu haka muna hanyarmu ta zuwa kauyen domin ganewa idanunmu abin da ya wakana. Zan tuntubeka idan na dawo,” inji kakakin.