✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun hallaka manoma 8 a Kaduna

Rahotanni sun ce an kashe su ne lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu.

’Yan bindiga sun hallaka akalla manoma takwas a kauyukan Buruku da Udawa da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce an kai wa manoman hari ne lokacin da suke tsaka da aiki a gonakinsu.

Kauyukan biyu dai na kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari wacce ta sha fama da hare-hare a baya.

Wani mazaunin yankin kuma shugaban al’umma, Muhammad Umar ne ya tabbatar wa da wakilin Aminiya haka ranar Asabar.

“An hallaka manoma biyar a garin Buruku, sai uku kuma a Udawa. Mun gaji da binne mutanen da ake kashewa a kullum, muna bukatar a agaji,” inji shi.

Da wakilinmu ya tunutbi kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwara harin, ko da yake ya ce ba su kai ga tantance hakikanin adadin mutanen da aka kashe ba.