A jihar Binuwai, wasu ’yan bindiga sun hallaka wani basaraken gargajiya, Cif Hyacinth Ajon da karin wasu mutum uku a hare-hare guda biyu a Kananan Hukumomi biyu na jihar.
Basaraken dai, a cewar rahotanni an kashe shi ne tare da wani mai suna Benjamin Anakula a gundumar Tse Zoola dake Karamar Hukumar Makurdi, yayin da wasu mutum biyu kuma da ba a bayyana sunansu ba aka kashe su a yankin Guma na jihar.
Wani dattijo a yankin, Aho Zoola, ya yi ikirarin cewa ’yan bindigar sun kai harin ne kan kauyukan da misalin karfe 2:00 na dare, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi har suka hallaka mutane biyun.
A cewar dattijon, ta bakin wani hadimin Gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya ce harin ya zo wa al’ummar yankin da ba-zata kasancewar ba su taba samin wata matsala da maharan ba.
Hadiminm Gwamnan, Jimmin Geoffrey, ya ce sai da Ortom din ya tsaya lokacin da yake dawowa daga wani bikin binne gawa domin jajantawa mazauna yankin.
Daga nan sai ya basu tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a girke musu jami’an tsaro domin kula da lafiyarsu.