Wadanda aka sacen sun hada da wata mace mai juna biyu da yara uku da manya hudu, kuma suna shafe sama da wata daya a hannun ’yan fashin bindigar.
Wani shugaban unguwar da bai so a bayyana sunansa ba, ya ce masu garkuwan sun yi barazanar kashe biyu daga cikin mutanen idan ba biya Naira miliyan 290 a kan lokaci ba.
Ya ce masu garkuwan sun bukaci “mu kawo Naira miliyan 290 cif kafin su sako su ko kuma su kashe biyu daga cikinsu.
“Sun bukaci mu kai musu buhunan shinkafa, kwalayen taliyar yara, maganin tari, maganin kashe kwayoyin cuta, zannuwan gado da rigunan sanyi.
“Sun kuma ce dole sai kudin fansan sun cika miliyan 290 kafin su sako mutanen manu da suka hada da mace mai ciki da yara uku,” in ji shi.
Ya roki Sufeto-Janar na ’yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, da Babban Hafsan Sojin Kasa, Janar Taoreed Lagbaja, da su kawo daukin wajen ceto wadanda aka yi garkuwa da sun.
A cewarsa, “Mun san cewa suna iya bakin kokarinsu amma muna rokon su da su kubutar da iyalanmu kamar yadda suka yi wa a kwanakin baya.
“Wasu daga cikin mutanen da aka sacen sun fara fama da rashin lafiya a hannun masu garkuwa da su,” in ji shi.