✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HOTUNA: Yadda aka kaddamar da Askarawan Zamfara 2,600

Rundunar na da jami'ai sam da 2,600 da suka hada da mata, domin yakar ’yan bindiga

Gwamnatin Zamfara ta kaddamar jami’an tsaronta da ake kira Askarawan Zamfara da nufin yaki da ’yan bindiga da sauran masu aikata laifi a jihar.

Gwamna Dauda Lawal Dare ya ce  rundunarm mai suna CPG tana da  dakaru 2,645, wadanda za su rika taimaka wa jami’an tsaro wajen yakar kalubalen tsaron da ke addabar jihar.

Ya shaida wa taron kaddamar rundunar cewa gwamnatin ta ba da muhimmanci kuma ta ware  kudade domin tsaron jihar, don haka ya kira ya bukaci jami’an da su ba da gudunmawa da ta dace wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma kawo karshen ayyukan ’yan bindiga a Zamfara.

Gwamnatin jihar ta sama wa jami’an na CPG motoci da babura da sauran kayayyaki domin gudanar da ayyukan nasu.

A jawabinsa, Gwamna Umaru Dikko Radda na Jihar Katsina ya jaddada shirin gwamnatocin Arewa ba magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki da ke ce wa yankin tuwo a kwarya.

Tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkokin Tsaro kuma tsohon ministan tsaro, Janar Aliyu Muhmmad Gusau, ya bayyana cewa yaki da matsalar tsaro na bukatar samar da nagartattun tsare-tsaren inganta rayuwa da tattalin arzikin jama’a.

Ali Gusau ya bayyana cewa, yawancin masu aikata manyan laifuka suna yi ne saboda zaman banza talauci a tsakanin matasa.