An kai wa wasu masu zaman makoki hari inda aka hallaka da dama daga cikinsu a daren Lahadi, a wani kauye da ke Jihar Inugu da ke Kudancin Najeriya.
’Yan bindigar da har yanzu ba a san ko su wane ne ba sun shammaci al’umar Nimbo ne da ke Karamar Hukumar Uzo-Uwani a jihar.
An kai harin ne a yammacin ranar Lahadin da ta gabata, inda wasu kuma suka tsira da munanan raunuka.
Wata majiya mai tushe ta ce maharan sun kai farmakin ne a kauyen Ugwuijoro da ke yankin Nimbo, inda suka far wa ‘yan gari da bakin da suka zo zaman makoki cikin sabon tashin hankali.
Wani bidiyo mai da ke nuna yadda abin ya faru da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta a safiyar Litinin ya nuna yadda garin ya zama kufai, saboda mutanen cikinsa duka sun tsere.
Sautin muryar wani a cikin bidiyon na bayyana firgici sakamakon yadda maharan suka kai harin ba tare da jama’ar garin sun yi aune ba.
An ce da isar maharan, ba su yi wata-wata ba suka fara harbi kan mai uwa da wabi a wurin zaman makokin.
An taba kai wani mummunan hari a wnnan kauye na Nimbo a shekarar 2016, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
Mummunan lamarin da ya faru a wancan lokacin ya jawo ce-ce-ku-ce sosai.
Kawo yanzu, duk kokarinmu ta jin ta bakin Kakakin ’Yan Sanda a Jihar Inugu, DSP Daniel Ndukwe, ya ci tura.