✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara

Tuni aka yi jana'izar jami'an da suka rasu a ranar Lahadi.

Aƙalla jami’an rundunar tsaron al’umma ta Zamfara (CPG) 10 ne, suka rasu, yayin da wasu 14 suka jikkata a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a yankin Anka da ke Jihar Zamfara.

Sun kai harin ne a ranar Asabar bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki wani sansanin ’yan bindiga da ke dajin Bagega a ranar Juma’a da Asabar.

A yayin farmakin, sun kashe ’yan bindiga da dama kuma sun kuɓutar da wasu mutanen da aka sace a sansanin wani ƙasurgumin shugaban ’yan bindiga, Alhaji Beti.

Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun kuma ƙone gidan wani shugaban ’yan bindigar mai suna Bellon Kaura, wanda lamarin da ya fusata su.

“Kurakuran da suka yi shi ne komawa ta hanyar da suka bi a lokacin farmakin farko,” in ji wani shugaba a yankin Anka.

“’Yan bindigar sun tsere daga sansaninsu amma sun shirya tarko, sun yi kwanton-ɓauna, kuma suka buɗe wuta bayan jin ƙarar baburan jami’an tsaron.”

Harin ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro bakwai daga Anka da kuma uku daga Talata Mafara.

Sunayen waɗanda suka rasu sun haɗa da Shehu Lawali, Murtala Mesin, Ubandawaki Moda, Muhammad Want, Haruna Kwanar Maje, Ibrahim Ware Ware, Yusuf Ware Ware, Rabi’u Barbara, Lawali Dan Hassi Jangebe, da Badamasi Gima.

An yi jana’izarsu a Anka a ranar Lahadi, inda Gwamna Dauda Lawal ya halarta, tare da ɗaukar alƙawarin ci gaba da goyon baya wajen yaƙi da ’yan bindiga a jihar.