✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun bude wuta a kan ayarin Sarkin Birnin Gwari

’Yan bindigar sun bude wa ayarin wuta a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.

Wasu ’yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II.

Aminiya ta samu cewa maharan sun bude wa ayarin wuta ne a babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da Yammacin ranar Litinin.

Sai dai wani shaidar gani da ido ya ce Sarkin ba ya daya daga cikin motocin yayin da harin ya auku.

Direban Sarkin mai suna Umar Jibril wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kwatsama ba su yi aune ba maharan suka gindaya musu rassan bishiyu a kan hanya da zummar tsayar da su da karfin tsiya.

“Amma ba mu tsaya ba, ni suka hara saboda ni nake tuki amma Allah ya tsare ni harsashin da suka harbo bai same ni ba.”

Ya ce baya ga ’yan kananan rauni da ya ji sakamakon tarwatsewar gilashin motar, babu wanda ya ji rauni.

Birnin Gwari na daya daga cikin Kananan Hukumomin jihar Kaduna da hare-haren ’yan bindiga suka yawaita.

 Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Litinin wasu ’yan bindiga suka kai hari wata makarantar Firamare da ke garin Rama a Karamar Hukumar ta Birnin Gwari inda suka yi awon gaba da wasu dalibai da malamai.