Kimanin wata takwas da sace dalibai ’yan mata daga makarantar sakandiren FGC Birnin Yawuri a Jihar Kebbi, har yanzu akwai sama da 10 a hannun ’yan bindigar da suka sace su.
Hakan na faruwa ne duk da makuden kudaden fansarsu da aka biya da kuma yarjejeniyar musayar fursunonin da aka yi a lokuta daban-daban da masu garkuwar da su.
- Dalilin da tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa —Farfesa Darma
- NAJERIYA A YAU: Yadda daukar doka a hannu ke lakume rayuka a Najeriya
Sai dai wata majiya mai tushe ta tabbatar wa Aminiya cewa akwai akalla dalibai ’yan mata 13 da a yanzu haka ’yan bindigar suka aure su, wasu daga cikinsu ma har sun samu juna biyu.
A ranar 17 ga watan Yunin 2021 ne dai ’yan bindigar, wadanda yaran Dogo Gide ne, suka far wa makarantar sannan suka sace dalibai da dama da malamansu biyar.
Aminiya ta kuma gano cewa tsakanin 11 zuwa 14 daga cikin daliban har yanzu suna hannun Dogo Giden, kuma namiji daya ne kawai a cikinsu.
Kimanin makarantu 10 ne ’yan bindiga suka kai wa hari a shekarar 2021 a jihohin Zamfara da Kaduna da Neja da kuma Kebbi.
Hare-haren tare da satar daliban sun biyo bayan wanda wani kasurgumin dan bindiga mai suna Auwal Daudawa ya fara jagoranta a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Kankara a Jihar Katsina a watan Disambar 2020, inda suka sace dalibai sama da 200.