’Yan bindiga sun yi garkuwa da wata Kwamishinar Kasa, Hukumar Kidaya ta Kasa a Jihar Bayelsa, Misis Gloria Izonfuo
’Yan bindigar sun bukaci a ba su Naira miliyan 500 kafin su sako Misis Gloria, wadda suka yi garkuwa da ita tare da ma’aikatanta guda biyu.
- Yakin Sudan: ’Yan Najeriya miliyan 3 ne a Sudan —Abike
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Jinkirin Kwaso ’Yan Najeriya Daga Sudan
An sace Misis Gloria Izonfuo, wadda tsohuwar shugabar ma’aikatan Jihar Bayelsa ce a Jihar Ribas, ranar Lahadi a hanyarta ta zuwa yankin Brass na jihar Bayelsa, daga Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Maharan sun yi awon gaba da ita ne tare da direbanta da dan aikinta, kamar yadda kakakin ’yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko ta tabbatar.
Ta ce kwamishinan ‘yan sanda jihar ya tura runduna ta musamman domin ceto mutanen.