’Yan bindiga na neman Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansar dalibai 39 da suka yi garkuwa da su daga Kwalejin Gandun Daji ta FCFM da ke Afaka Kaduna.
Wasu iyayen daliban da aka yi garkuwa da su sun tabbatar cewa ’yan bindigar sun tuntube su suna neman kudin fansa Naira miliyan 500.
’Yan bindigar sun kuma fitar da bidiyon da ke nuna halin da daliban suke ciki a hannunsu a cikin daji.
A bidiyon, daliban, maza da mata kuma yawancinsu babu riga a jikinsu, sun yi bayani suna rokon Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna su cece su, tare da cewa ’yan bindigar na neman kudin fansa N500m.
Masu garkuwar sun fitar da bidiyon ne ta da shafin Facebook na wasu daga cikin daliban sa’o’i kadan bayan garkuwa da su.
Wasu daga cikin daliban kwalejin da suka kubuta daga harin sun tabbatar cewa wadanda ke cikin bidiyon ’yan makarantar ne.
Mun yi kokarin jin ta bakin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, kan halin da ake ciki amma hakarmu ba ta cimma ruwa ba.
Sai dai a hirar da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi watsi da batun biyan kudin fansa don kubutar da daliban.