Iyayen dalibai 29 na Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya dake Afaka a jihar Kaduna da suka rage a hannun ’yan bindiga sun ce ana musu barazanar kashe maza da kuma auren matan da suke hannunsu.
Aminiya ta rawaito cewa bayan sace dalibai 39 daga Kwalejin, ’yan bindigar sun sako 10 daga cikinsu a makonni biyun da suka gabata.
- Turkiyya ta haramta amfani da kudaden Cryptocurrency
- Warwara da nade-naden sarautu bayan rasuwar Sarkin Zazzau
- ’Yan sa-kai sun aika ’yan bindiga lahira a Kasuwar Dansadau
Bakwai daga cikin 10 na daliban maza ne yayin da ragowar ukun kuma mata ne.
’Yan bindigar dai sun bukaci Gwamnatin Jjhar Kaduna ta biya su Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansar daliban, ko da yake Gwamna Nasir El-Rufai ya sha alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan bindiga ba ballantana ta ba su ko sisi a matsayin kudin fansa.
Gwamnan ya kuma yi barazanar cewa gwamnatin za ta kama duk wanda ya shiga sulhu da ’yan bindigar a madadinta.
Jin hakan ne dai ya sa ‘yan bindigar suka fara neman iyayen daliban da suka rage a hannunsu suna neman su basu kudaden fansar ’ya’yansu, wanda ta haka ne dalibai 10 da aka sako suka sami shakar iskar ’yanci.
Sai dai a wani taron manema labarai da iyayen daliban suka gudanar a makarantar a ranar Juma’a, sun bukaci ’yan Najeriya da su taimaka su yi musu kudi-kudi don su samu su kubutar da ’ya’yan nasu daga hannun ’yan bindigar.
Iyayen sun ce ko kadan basu razana da barazanar Gwamnatin jihar ta kamawa da tsare duk wanda ya yi yunkurin sulhu da ’yan bindigar matsawar yaran nasu za su kubuta.
Sakataren Kungiyar Iyayen Daliban Kwalejin, Friday Sanni ya ce, a matsayinsu na iyaye yanzu haka ba su da wani zabi face su biya kudaden fansa a sako musu ’ya’yan nasu.
Ya ce, “Muna rokon ’yan Najeriya da kungiyoyin da ba na gwamnati ba da kungiyoyin jinkai da su taimaka mana don a kubutar da yaranmu.
“Ba mu san halin da suke ciki ba, ’yan bindiga na yi mana barazanar za su kashe su idan muka yi musu wasa da hankali.
“Sun ma ce za su aure ’yan matan daliban su kuma kashe mazan cikinsu, kuma idan aka kai wannan lokacin, ko mun ba su kudaden ba za su yi amfani ba,” inji shi.
Sanni ya ce, tun lokacin da gwamnati ta bayar da shelar jami’an tsaro sun yi nasarar kubutar da rukuni biyu na mutum 10 daga cikin daliban, me zai hana su ma ragowar a kawo musu makamancin wannan agajin.