✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga ke lalata wutar lantarkin Najeriya —Gwamnatin Tarayya

Ko an gyara wutar ’yan ta’adda na zuwa su sake lalatawa

Gwamnatin Tarayya ta ce ’yan ta’adda ke dakile kokarinta na samar da wadatacciyar wutar lantarki ga ’yan Najeriya, musamman ma a yankin Arewa maso Gabas.

Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa a yankunan Arewa maso Gabas, da Arewa ta Tsakiya, da Arewa ta Yamma, ’yan bindigar ne suka lalata kayayyaki da tashoshin wutar, kuma bayan an gyara suka sake lalatawa.

Ya ce don haka yanzu dole gwamnati ta bullo da wasu hanyoyin samar da wutar lanatarkin ko da ba su kai inganci da saukin na baya ba, musamman ma a garin Maiduguri da ke Jihar Borno da abin ya fi muni, domin jawo musu wutar lantarkin ta karamar ta Damaturun Jihar Yobe.

“Yanzu dai mun dawo da dan kwangilar domin ya gyara wacce aka lalata a kwanakin baya.

“In dai muna son ba wa Damaturu da kewaye wadatacciyar wutar lantarki har mu kai ta Maiduguri, sai mun kara karfi da ingancin karamar tashar wutarsu”, in ji shi.

To sai dai ministan ya ce jami’ansu ba su sami shiga Jihar Neja da yankin Shiroro da ke Arewa ta Tsakiya ba, domin ganin ko tashohin wutar lantarkin ne suka lalace a can ko a’a, sakamakon faman da yankunan suke da matsalar tsaro.

Amma ya ce duk da hakan jami’ansu na tattaunawa da bangaren tsaro, domin lalubo hanyoyin da suka dace su bullowa lamarin.

Ministan ya yi wannan bayanin ne bayan Gwamnatin Tarayyar ta sahale aiwatar da wasu kwangiloli a bangaren samar da wutar lantarki da ruwan sha, wandda za su lakume fiye da Naira biliyan 23.

Ya yi jawabin ne bayan kammala taron Majalisar Zartaswa da ta Kasa, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.