✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga 15 sun kwanta dama yayin artabu da sojoji a Neja

’Yan bindigar wanda adadinsu ya kai saba’in sun mamaye yankin a garin Kontagora.

Akalla ’yan bindiga 15 ne suka kwanta dama yayin wani artabu da dakarun soji a Unguwar Mallam da ke garin Kontagora a Jihar Neja.

Aminiya ta samu cewa, wani jami’in soji daya ya riga mu gidan gaskiya yayin musayar wuta da ’yan ta’addan a ranar Asabar.

Majiyoyi daga yankin sun ce lamarin ya faru ne da misalign karfe 4 na yammacin ranar Asabar yayin da sojojin da ke sintiri a Unguwar Mallam suka hangi maharani daf da garin Kontagora.

Sojojin yayin sintiri sun yi kacibus da gawarwakin mutane a cikin jeji da kuma shimfidun kwanciya na ’yan bindigar.

Mazauna sun ce sojojin sun tunkari ’yan bindigar wanda a sandiyar haka ne suka samu nasarar kashe da dama daga cikinsu, sai dai soja daya ya ransa.

Bayanai sun ce ’yan bindigar wanda adadinsu ya kai saba’in sun mamaye yankin, sai dai dakarun sojin da aka jibge ya hana su wani yunkuri na kai wa al’ummar yankin hari.

Sai dai har yanzu rundunar ’yan sandan jihar ba ta ce uffan ba a kan lamarin.