Shugaban Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Ango Abdullahi, ya soki jayayyar da wadanda ya kira ’yan barandar siyasa da ya ce su ne matsalar Jam’iyyar PDP alhali ba su san yadda aka kafa jam’iyyar ba.
Farfesa Ango Abdullahi ya ce su ne suka kafa Kungiyar G6 wadda ta rika fadada har zuwa G34 da nufin dawo da mulkin farar hula a Najeriya daga mulkin soja.
- NAJERIYA A YAU: ’Yan Kudu sun mayar da mu abin kashewa a yankinsu —’Yan Arewa
- Sarkin Kano ya je ta’aziyyar Sarauniyar Ingila
Ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a gidansa da ke Zariya a karshen mako.
Ya ce ganin yadda alamu suka nuna, wasu sojoji na da sha’awar rikidewa zuwa farar hula domin ci gaba da mulki kamar yadda marigayi Janar Sani Abacha ya nuna sha’awarsa.
Haka kuma ya ce a lokacin da jam’iyyun da suka nemi rajista da yawa daga cikinsu ba a yi masu rajista ba kamar jam’jyyarsu ta PDM da wasu manyan jam’iyyu don gudanar da harkokin siyasa ya sa suka kafa kungiyar.
Farfesa Ango ya ce a wancan lokaci an yi wa kananun jam’iyyu rajista da nufin in sun zo gudanar da babban taron da za su fitar da dan takarar Shugaban Kasa sai su tsayar da Janar Abacha, kuma hakan ya faru in ban da Jam’iyyar GDM wadda marigayi Alhaji M.D. Yusuf ke jagoranta wadda ta ki amincewa da tsarin.
Shugaban Kungiyar NEF ya ce ganin abin da ya faru dole ya sa masu sha’awar siyasa suka tattara hankalinsu waje daya suka kafa Jam’iyyar PDP wannan shi ne asalin yadda aka kafa PDP daga kungiyar PDM wadda marigayi Shehu Musa ’Yar’aduwa ya assasa.
Ya ce wadanda suka kafa PDP su ne marigayi Alhaji Abubakar Rimi da marigayi Lawal Kaita da Solomon Lar da Yahaya Kwande da Isiyaku Ibrahim da Barnabas Gemade da Jibril Aminu da Bamanga Tukur da Sani Zangon Daura.
Sauran su ne, Olusola Saraki da Anthony Anenih da Musa Musawa da Atiku Abubakar da Jerry Gana da Sule Lamido da Iyorchia Ayu wanda Nyesom Wike, ke jayayya da shi a kan rashin sani.
“Kamar G6 da G8 da G18 duk ’yan Arewa zalla ne suka fara kuma a G18 ne aka dora Solomon Lar ya shugabanci G18,” inji shi.
Farfesa Ango ya ce daga G18 ne suka fadada kungiyar zuwa ta kasa gaba daya inda aka sanya Cif Aled Ekweume ya zama Shugaban G36.
Duk da wannan gwagwarmayar da aka sha daga cikin wadanda suka kafa Jam’iyyar PDP da dama sun yi ta tsalle daga wannan jam’iyyar zuwa waccan.
Farfesa Ango ya kalubalaci dukkan tsofaffin gwamnoni da na yanzu wadanda ya kira ’yan barandan siyasa cewa a lokacin da suka kafa Jam’iyyar PDP babu wanda ya isa ya matso inda suke, sai ga shi yanzu suna ta kokarin bata tsarin saboda son zuciya.
Shugaban Kungiyar Dattawan Arewar ya yi kira ga ’yan Najeriya su sa natsuwa domin hana ’yan barandar siyasa ci gaba da mulkar su.