Cima kwance kalma ce, da masana suka yi bayanin ta a matsayin mutum wanda baya iya tashi domin dogaro da kansa wato (raggo), wanda kuma mafi akasarin mazauna kudancin qasar nan ke furta kalmar ga ‘yan arewa.
Wannan kalmar ta cima kwance da ake kiranmu ‘yan Arewacin Najeriya da ita, ta daxe tana ciman tuwo a qwarya, ganin irin albarkatun qasa, kama daga qasar noma da ma’adanan qasa da kuma ximbin baiwa da basira da ‘yan arewa ke da, wanda har akwai ximbin fitattun mutane da suka yi fice wanda duk daga Arewacin Najeriya.
Ba komai ya sa suke furta kalmar ba, face yadda muke da son kai, da kuma rashin xaukar qaramar sana’a da muhimmanci, musamman a birane, da matashi zai kammala karatu, daga matakin sakandare, har zuwa makarantun gaba da sakandare, da za ka ga mutum ya kammala difloma, ko NCE, koma digiri, amma ya zauna a gida da nufin sai ya samu aikin ofis, da zai ji daxi cikin qankanin lokaci, wanda ta dalilin
hakan ne, ya janyo rashin ayyukkan yi a tsakanin matasa, da ‘yan kudancin qasar nan ke kira ‘yan arewa da cima kwance.
A tarihin Najeriya, Arewa ta taka gagarumar rawa, wajen samar da quxin shiga ga Najeriya, kama daga gida da ake nomawa daga Arewa, da sauran abubuwan noma da ake samarwa daga Arewa, da duk sauran albarkatun qasa, kama daga zinari, wanda aka soma aiwatar da muhimman ayyukkan ci gaban Najeriya.
Wanda kuwa akwai ximbin qananan sana’o’i da za mu iya dogaro da su, domin biyan buqatocin mu, ‘yan Arewa sun taka gagarumar rawa wajen ciyar da Najeriya da ‘yan Najeriya a gaba, tun a zamanin shugabannin da suka karvo wa Najeriya ‘yan cin kanta, kama daga ‘yan Arewa da suka shugabanci Najeriya, irin Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Sir Abubakar Tafawa Valewa da Malam Aminu Kano da Shehu Shagari da Muhammadu Buhari da Janar Murtala Muhammed da Sani Abacha da Ibrahim Badamasi Babangida da Abdussalami Abubakar da Umaru Musa ‘Yar Aduwa, duk ‘yan Arewa ne, da suka taka gagarumar rawa, wajen kawo sauyi a Najeriya da kuma irin manyan ‘yan kasuwar da muke da su, musamman Aliko Xangote, wanda
ya yi fice a duk faxin duniya a sha’anin kasuwanci, wanda dukkanin kamfunansa a kudancin Najeriya suke, da masu yimana kallon cima kwance, suke amfana wajen karbar haraji da kuma samun kuxin shiga ga gwamnatocin da ke jihohin da kamfunan suke, da kuma samarwa matasan yankin da ayyukkan. yi, da kuma ximbin ‘yan Arewa da suka yi fice a fannin kasuwanci, noma, kiwo, kimiyya da fasaha, da sauran fannonin da mu ‘yan Arewa mukayi fice a Najeriya, da duniya baki xaya.
Hakazalika a fannin yawan jama’a Arewa mu ne kan gaba wajen yawan al’umma, a Najeriya wanda samuwar al’umma na tafiya ne dai-dai da ci gaban yankin. Sai dai abin tambaya a nan, wane dalili ne ya sa suke kiran mu, da kalmar “cima kwance”, a iya nazari da binciken da na gudanar, ya nuna cewa rashin yin qananan sana’o’i, ga matasan mu na Arewa, musamman irin, kafinta, walda, kanikanci, kiwo, noma, da a kullum zaka riqa ganin matashi yakai munzalin xaukar dawainiyar iyayensa, amma saboda rashin xaukar sana’a da muhimmanci, iyayen sa za su cigaba da xaukar dawainiyarsa, na makaranta, abinci, dama sutura, musamman idan matashi ya yi karatun boko, to fa shi burinsa, ya zamo ma’aikacin gwamnati, ko kamfani, mai ofis da zai riqa wuni cikin jin daxi, wanda halin da muke ciki a Najeriya, matasa na fuskantar qalubalen rashin ayukkan yi, da kuma ba sa iya rungumar karamar sana’a, da wannan ya zama sillar yawaitar dubban matasa marasa ayyukkan yi, a Najeriya wanda galibi matsalar tafi kamari a Arewa, da ya zama dalilin kiran mu ‘yan arewa da ‘yan kudancin qasar nan keyi da cima kwance.
Wannan ya sa nake qara janyo hankulan ‘yan uwana matasa, musamman na Arewa da mu farka daga barci, kamar yadda marigayi Dokta Mamman Shata, ke faxa a cikin baitinsa “ku tashi mu farka ‘yan Arewa, musan barci aikin kawai ne”, mu tashi mu dukufa wajen rungumar qananan sana’o’i, da kuma sana’o’in hannu, tun daga na gargajiya, waxanda muka gada tun kaka da kakan, da kuma rungumar na zamani, musamman zamu iya rungumar na gargajiya, mu sarrafa su domin su tafi dai-dai da zamani, da kuma na zamanin, haka akwai buqatar makarantun gaba da sakandari su riqa bawa xalibai ilimi a zahiri, bawai karatu a zahiri kaxai ba, ta yadda za su iya amfani da ilimin da suka sama, domin kasuwanci domin dogaro da kai, misali idan ka karanci Kwamfuta ya zama na kanada qwarewar iya aikin bizines santa, domin yin foto kwafi, laminashin, ko kuma idan fannin yada labarai (Mass Kwaminikeshin), ka karanta ya zama kana da qwarewa kan xaukar hoto, da shi ma zai taimaka domin dogaro da
kai. A vangaren gwamnati, da sarakunan gargajiya, ya kamata su fito da shirye-shirye domin matasa, da kuma faxakar da ‘yan Arewa, muhimmancin sana’a, musamman ta hannu da
kuma qananan sana’o’i, ta hanyar shirya tarukkan qarawa juna sani, da faxakarwa ta hanyar kafafen yaxa labarai, wajen shirya talla da kuma tallafawa da jari ga matasan, da zai sa mu farka daga barci, mu kawar da kalmar “Cima Kwance”, da ake kiran mu da ita, domin mukasance ma su alfahari da yankin mu na Arewa.
Za a iya tuntuvar Malam Aminu a [email protected]