Gamayyar ’Yan Arewacin Najeriya mazauna kasar Amurka mai suna Dangi USA, ta bukaci gwamnati kada ta yi sulhu da ’yan bindiga.
Gamayyar ’yan Arewan ta ce hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa na babu gaira, babu dalili, ya sa babu bukatar a ba su damar yin sulhu.
- An sace dan sandan da ke sashen yaki da garkuwa da mutane a Adamawa
- Najeriya A Yau: Sakacin gwamnati ne silar kai hari a makarantu A 2021
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Kabir Isa Jikamshi ya fitar, inda ya ce kamata ya yi gwamnati ta fatattake su.
“Babu wata maganar sulhu da za a yi duba da yadda suka jefa rayuwar mutane cikin tsaka mai wuya. Don haka babu wanda zai shiga maganar sulhu daga tsagin gwamnati ko kungiyoyi.
“Muna kiran gwamnati da ta tuna karfinta da kuma sauke nauyinta na kare rayuka da dukiyar al’umma. Matsalar tsaro na ta’azzara ne idan gwamnati ta gaza yin katabus, don haka yana da kyau gwamnati ta jajirce.
“Ya kamata gwamnati ta shiga yaki da ’yan bindiga sannan ta kafa da duk wata doka da za ta taimaka wajen kawo murkushe su.
“Abin bakin ciki ne ne yadda ake kashe mutane, ake karbar kudaden fansa, ake sace kananan yara da mata, musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya,” a cewar sanarwar da suka fitar.
Gamayyar ta yi nuni da cewa sulhun da aka yi a baya da wasu ’yan bindiga musamman a jihohin Katsina da Zamfara bai haifar da sakamako mai kyau ba.
Sun kuma soki yadda ake sakin wasu ’yan bindigar ba tare da an hukunta su ba, wanda suka ce hakan zai ci gaba da haifar tasgaro ga kokarin da ake yi na samar da tsaro.