Ministan Ilimi, Adamu Adamu ya zargi ’yan Arewacin Najeriya da zama musabbabin yaduwar jahilci a yankin.
Ministan ya ce duk da cewa ’yan Arewa na bugun kirji da addinin Musulunci wanda ke karfafa neman ilimi, amma kuma su ke yi wa harkar neman ilimi manakisa.
- Ainihin dalilin ganawar Tinubu da Kwankwaso da Sanusi II a Faransa
- DAGA LARABA: Yadda Hausawa Ke Shiga kungiyoyin Asiri A Kudu
Ya ce, idan ba haka ba, jami’o’i biyu na farko a duniya mata Musulmi ne suka kafa su, amma kuma wasu a Arewa na “fakewa da Musulunci suna hana mata fita neman ilimi.”
Ministan ya yi wannan furuci ne a taron kaddamar da manhajar karatun jami’o’i da wani littafi a kansa da Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta gudanar a Abuja.
Ya jinjina wa NUC bisa kokarinta na kafa sabbin jami’o’i a Najeriya, musamman yadda a baya-bayan nan da akasarin sabbin jami’o’i da hukumar ta ba wa lasisi a yankin Arewa suke.
A ranar Litinin Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da ba da lasisi ga wasu sabbin jami’o masu zaman kansu guda 37 kuma yawancinsu a Arewaci suke
Adamu ya ce an kaddamar da sabon manhajar karatun jami’o’in ne domin tabbatar da ilimin jami’o’i a Najeriya ya dace da zamani.
Don haka ya yi kira da a yi duk mai yiwuwa wajen sama musu wadatattun kayan aiki domin cimma wannan hadafi.
Ya kuma yi kira da a kafa hukumar kula da aikin koyarwa domin inganta harkar ilimi.
Da yake nasa jawabin, Shugaban NUC, ya ce a halin yanzu jami’o’i 148 masu zaman kansu ne a Najeriya kuma 87 (kashi 60%) daga ciki an kafa su ne a zamanin Minista Adamu Adamu.