✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Arewa a Majalisar Tarayya sun ba da gudummawar N395m

’Yan Arewa a Majalisar Wakilai sun ba da gudunmmawar kudi Naira miliyan 45 da kayan more rayuwa na miliyan 350 ga al'ummar kauyen Tudun Biri

’Yan Arewa a Majalisar Wakilai sun ba da gudunmmawar Naira miliyan 45 da kayan bore rayuwa na miliyan 350 ga al’ummar kauyen Tudun Biri da jirgin soja ya kai wa harin a taron Mauludi a bisa kuskure.

Shugaban ’Yan Arewa a Majalisar, Alhassan Ado Doguwa ya sanar da alkawarinsu na samar da abubuwan more rayuwa da kudinsu ya kai Naira miliyan 350 a kauyen.

Doguwa ya ce abubuwan da za su samar sun hada da cibiyar lafiya, azuzuwan makaranta da rijiyar burtsatse da kuma dakin taro.

Ya kara da yin Allah-wadai da harin, tare da cewa sun yanke shawar kai ziyarar ta’aziyya Tudun Biri.

Ya sanar da gudummawar ne a sakon jajensu ga al’ummar kauyen a zauren majalisar a ranar Litinin.

Dan majalisar ya bayyana cewa ziyarar za ta ba su damar gane wa kansu don fahimtar ainihin abin da ya faru a harin da jirgin sojin ya kai.

Sun ba da gudunmmawar ne washegarin da sanatoci 109 gaba dayansu suka ba wa al’ummar da harin ya shafa gudunmmawar miliyan N109.