’Yan Arewa a Majalisar Wakilai sun ba da gudunmmawar Naira miliyan 45 da kayan bore rayuwa na miliyan 350 ga al’ummar kauyen Tudun Biri da jirgin soja ya kai wa harin a taron Mauludi a bisa kuskure.
Shugaban ’Yan Arewa a Majalisar, Alhassan Ado Doguwa ya sanar da alkawarinsu na samar da abubuwan more rayuwa da kudinsu ya kai Naira miliyan 350 a kauyen.
Doguwa ya ce abubuwan da za su samar sun hada da cibiyar lafiya, azuzuwan makaranta da rijiyar burtsatse da kuma dakin taro.
Ya kara da yin Allah-wadai da harin, tare da cewa sun yanke shawar kai ziyarar ta’aziyya Tudun Biri.
- Rikicin Siyasa: ’Yan majalisa 27 sun sauya sheka daga PDP a Ribas
- ’Yan sanda sun kashe ’yan ta’adda da ke neman sace matafiya a Katsina
Ya sanar da gudummawar ne a sakon jajensu ga al’ummar kauyen a zauren majalisar a ranar Litinin.
Dan majalisar ya bayyana cewa ziyarar za ta ba su damar gane wa kansu don fahimtar ainihin abin da ya faru a harin da jirgin sojin ya kai.
Sun ba da gudunmmawar ne washegarin da sanatoci 109 gaba dayansu suka ba wa al’ummar da harin ya shafa gudunmmawar miliyan N109.