Akan kira su ’yan Achaba, ko ’Yan Haya da Babura, ko ’Yan Arubza, ko ’Yan Okada ko ’Yan Going, da dai sauransu. Yawancinsu matasa ne da suke daukar jama’a kan babura, daga wannan wuri zuwa wancan don neman na rufin asiri, ko a birane ko a karkara. A yanzu, a yawa-yawan wuraren da suke gudanar da sana’ar tasu, sukan hada kai don yi wa juna taimakon gaggawa duk yayin da hakan ta taso. Aminiya ta zagaya, ta tuntubi wasunsu, kuma ta yi nazari da sharhi dangane da sana’ar tasu kamar haka:
Ana samun su a yawancin biranen kasar nan, wadansu biranen kuma an haramta su, kamar a Abuja da Ikko da Kano da sauransu. A Kaduna, inda na mayar da hankali shi ne Dandalin Murtala, inda na samu yin nazarin yadda suke gudanar da tasu sana’ar:
Wadannan masu sana’a, akwai masu ganin farinsu, akwai kuma masu ganin bakinsu, kamar yadda ake yi wa dakaru kirari, wato kowa ya ga farinku, lallai zai ga bakinku. Na daga cikin ababen yabon, suna taimaka wa kansu-da-kansu don sun guji zaman kashe wando, ko na dumama-benci, domin a cikinsu akwai masu ilimi tun daga digiri har zuwa kasa. Suna tallafa wa jama’a, wadanda ba za su iya daukar hayar motar tasi ba. Sun san hanyoyin garin da suke chabawar a cikinsa, ta yadda sukan tallafi bako su kai shi inda yake son zuwa. Suna kuma sayar da ransu don bin bata-gari, misalin wadanda suka saci mota ko babur ko fizgen jakar bayin Allah da suka fito daga banki, misali.
Ana iya danganta su da ‘kuruci-dangin-hauka’, in an yi la’akari da yadda suke kasada yayin da suke dauke da mutane ko yaran makaranta, ta yadda suke shiga tsakankanin motoci a guje, duk don zalamar neman kudi.
Sana’ar achaba ta samu karbuwa ne lokacin da siyasa ta kankama tun a shekarar 1999 yayin da matasan da suka sami babura suka rika barazanar sun dara-dangi don suna da ubangida a gwamnati, suna da abin samun kudi.
A jihohin da aka haramta achaba, matsaloli ne da suka taso, domin sun fara zama annoba, domin sauran masu ababen hawa, musamman motoci, sun lura ba sa yin la’akari da dokokin hanya saboda irin mugun gudun da suke yi da kin amfani da sigina, sai dai su sa hannu ko ma kafa, wasu ba su da lamba, ba hular kwano, ko kuma a sa koren roba a rufe lambar. In ma har aka yi rashin sa’a, sai a samu ana cikin kwaya, ko an sha zakami da dai sauransu daga cikin kayan maye. Sannan ga taron-dangi, wanda da yawa ba adalci a cikinsa, in wani daga cikinsu ya yi hatsari da mai wani abin hawan daban. Wadannan dabi’u da wadansu munanan da ba a son fadi, na daga cikin dalilan da mai hankali zai ga bakinsu.
A Kaduna, jami’an kula da ababen hawa “B.I.O”, sun fara tilasta musu sayen lambar shaida watau ‘ID Card’ don a san mutum yana da adireshi, idan ya sami hadari, misali.
A Dandalin Murtala, daya daga cikin mattatarar ’yan achaba, akwai alamar, tare da yin karin kwaskwarima ga sha’anin, ana iya samun kykkyawan misali na koyi don kyautatuwar lamari a sana’ar. Sukan yi adashin-gata don taimakon wanda ya cimma kaddarar hadari ko kuma aka yi masa haihuwa ko wanda ya yi shirin aure.
Na sami tattaunawa da daya daga cikin jami’an wurin, mai lakanin “A taimaki al’umma” wato Malam Aminu Muhammad, wanda kuma aka fi sani da ‘Yello’, mazaunin Kawo. Ya shaida wa Aminiya cewa sun kai shekara tara suna wannan hadaka. Sannan suna da shugabansu Isyaku Umar, wanda ake wa lakabin ‘Ya-haji’, wanda ke tsawata da a daina ganganci; a yi wa baki fada su fahimci gari kafin su fara chabawa.
Ya ce hadin kansu ya sa suna taro kowace Lahadi don yin karo-karon da suke rika tallafa wa junansu. “Mukan gudanar da lamuranmu, a nan, a kan tsari, gwargwadon hali. Muna tsawata wa juna, wajen yin abin da ya kamata, kuma duk wanda ya zo nan, lallai ne a san shi, saboda gudun bata-gari. Muna iyakar kokari wajen taimaka wa jama’a, musamman baki da muka lura suna cikin wata matsala, misali.
Jami’in tsawatarwa na kungiyar mai suna Malam Aliyu Garba Barakallahu ya ce a yanzu suna karo-karo ne don dayansu mai suna Abdullahi Dogo Rafin-Guza ya samu haihuwa. Ya ce sukan hada har Naira dubu goma don taimako. Sannan suna da Naira dubu goma a cikin asusun da suka kira na ko-ta-kwana.
’Yan Achaba: Masu sana’ar sufuri da ganganci ko…
Akan kira su ’yan Achaba, ko ’Yan Haya da Babura, ko ’Yan Arubza, ko ’Yan Okada ko ’Yan Going, da dai sauransu. Yawancinsu matasa ne…