Kungiyar matuka baburan haya na A Daidaita Sahu a Jihar Kano ta bayar da sanarwar janye yajin aikin da ta fara a ranar Litinin.
Masu baburan sun janye yajin aikin ne bayan wani zama da suka halarta, karkashin jagorancin babban lauya, Barista Mahmoud Gadanya, tare da Shugaban Hukumar Kula da Zirga-zigar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), Baffa Babba DanAgundi da kuma lauyan kungiyarsu, Barista Abba Hikima, a yamamcin ranar Laraba.
A yayin zaman, an cim-ma matsaya cewa, ’yan A Daidaita Sahun za su dawo bakin aikinsu a ranar Alhamis.
Kungiyarsu kuma za ta aike wa gwamnatin jihar a rubuce tare da neman ragin kudin sabunta rajistar lamban babura a kan N8,000.
Sannan za a jira matakin da gwamnatin jihar za ta dauka kafin ranar 18 ga watan janairun da muke ciki.
Zaman ya kuma amince cewa matuka baburan za su ci gaba da biyan harajin N120 da suka saba biya a kullum.
Matuka baburan hayan sun tsunduma yajin aikin ne a ranar Litinin, domin nuna adawarsu ga matakin da gwamnatin jihar dauka cewa sai sun sake sabunta rajistar lambar baburansu.
Yajin aikin dai ya jefa dubban mutane a jihar cikin tsaka mai wuya, lamarin da ya sa mutane da dama taka sayyadarsu saboda rashin baburan da za su kai su wuraren da za su.
Yanayin dai ya shafi harkokin kasuwanci, ma’aikatu, dalibai da sauransu.