✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zanga-zangar cire tallafin mai ke gudana a Najeriya

Ma'aikata na zanga-zanga kan matsin rayuwa da suka shiga a sakamakon tsare-tsare gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) na jagorantar zanga-zanga a fadin kasar domin adawa da matakan da gwamnati ta dauka na janye tallafin mai wanda ya haifar da tsadarsa da ma na rayuwa a fadin kasar.

A ranar da aka rantsar da Shugaban kasar ya cire tallafin mai, wanda ya sa farashin fetur tashi daga 197 zuwa 540 kafin daga bisani ya kai 620 cikin wata biyu. Haka kuma ya mayar da harkar canjin kudi mara kaidi, wanda hakan ya sa farashin Dala haura N800 a halin yanzu.

Amma da yake jawabi a game da zanga-zangar, tsohon shugaban NLC, Ayuba Wabba, ya ce, ba zai yiwu Najeriya ta bar farashin manta da na canji, yanayin kasuwa ya rika juya su ba.

Da farko NLC ta ce za ta iya tsahirtawa da zanga-zangar da ta shirya, domin jin abin da Shugaba Tinubu zai bayyana a jawabinsa ga al’ummar Najeriya ranar Talata. Amma bayan jawabin nasa ta bayyana cewa, bai isa hadiya ba, ballantana ya kashe kishirwa.

Ga dai yadda zanga-zangar ke gudana a jihohi daga wakilanmu.

Abuja

Tun da sanyin safiya aka girke jami’an tsaro a kan titunan Babban Birnin Tarayya domin tabbatar da doka da oda da kuma dakile duk wata barazanar tsare da ke iya tashi a yayin zanga-zangar ta NLC.

 

Kano

A Jihar Kano, tun da sanyin safiya ma’aikata sun yi tattaki daga titin Ahmadu Bello zuwa gidan Gwamnatin Jihar, inda Sakataren Gwamnati Abdullahi Baffa Bichi, ya tarbe su. Da farko ya ya kokarin lallashinsu su fasa tattakin, amma suka yi biris da shi.

 

Borno

Delta