✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba gudu ba ja da baya kan zanga-zanga ranar Laraba — NLC

Ƙungiyoyin sun ce sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi kan zanga-zangar.

Kungiyoyin Kwadago na NLC da TUC, sun ce zanga-zangar da suka shirya yi a ranar Laraba kan yaki da hauhawar farashin man fetur da sauran manufofin Gwamnatin Tarayya na nan daram.

Shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a daren Talata a Abuja.

Ya ce rahotannin da ke yawo a kafafen sadarwa na cewa kungiyar za ta dakatar da gudanar da shiga zanga-zangar ba gaskiya ba ne.

Tun da fari Aminiya ta rawaito Sakataren NLC na kasa na cewar NLC na iya dage zanga-zangar da ta shirya shiga a ranar Laraba.

Kungiyoyin dai sun shirya zanga-zangar ce don nuna rashin goyon bayansu ga abin da suka kira da “tsauraran manufofi tattalin arziki” na Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Sakataren kungiyar na kasa, Emma Ugbaja, ne ya bayyana hakan ga manema labaran Fadar Shugaban Kasa, bayan an dage tattaunawar da suka tsara yi da gwamnatin Tarayya a dakin taro na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

‘Ba abin da muka cim ma a tattaunawarmu da gwamnati’

Shugaban kungiyar, ya bayyana cewa taron da suka yi da wakilan Gwamnatin Tarayya bai sauya komai ba, inda ya umarci majalisun jihohin kasar da su tashi tsaye domin daukar mataki.

“Ba mu dakatar da zanga-zangar da ake shirin yi a fadin kasar nan ba, muna so mu sanar da daukacin ’yan Najeriya cewa mun tashi daga taron da muka yi da Gwamnatin Tarayya inda muka nemi ganin sun saurari bukatun jama’a da ma’aikatan Najeriya.

“Sakamakon wannan taro da aka yi a safiyar yau, duk da haka, babu abin da ya canza, ko tsarin da muka sanya wa kanmu gobe a matsayin masu kula da muradun ma’aikata da jama’ar Najeriya.

“An shawarci ’yan Najeriya da su yi watsi da labaran da ke yawo, muna kira ga kowa da kowa da ya taru a jihohinmu da kuma duk inda muke a fadin kasar nan don ba da gudunmuwa ga wannan kuduri na hadin gwiwa. Gobe za a fara zanga-zangar gama-gari a fadin kasar,” in ji Ajaero.

Kungiyar ta lissafta bukatunta da take muradin a cika su cikin gaggawa wanda suka rattabawa hannu tare da gwamnati da TUC da kuma “dawo da duk wasu manufofin gwamnati na yaki da talauci kamar karin kudin makaranta na manyan makarantun gaba da sakandare, farashin man fetur”.

Sauran bukatun sun hada da gyara matatun mai na gida a Fatakwal, Warri da Kaduna; sakin albashin malaman jami’o’i da ma’aikata na tsawon wata takwas; ba da goyon bayan da ya dace ga kwamitin gudanarwa na shugaban kasa da ayyukan kananan kwamitocinsa da kuma dakatar da wasu manufofin gwamnati.