✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda zaki ya kashe matashi a gidan zoo a Ghana

Matashin ya tsallaka katanga ya shiga cikin wurin aka killace zakuna

Wani matashi ya gamu da ajalinsa a hannun wani zaki ga gidan ajiyar namun daji a kasar Ghana.

Hukumar Kula da Gandun Daji ta Kasar Ghana ta ce a ranar Lahadi ne matashin ya gamu da ajalinsa jim kadan bayan ya tsallaka katangar gidan zoo din.

Ta ce jami’anta na tsaka da gudanar da sintiri a gidin zoo din da ke Dajin Achimota da ke yankin birnin Accra ne suka hango matashin ya tsallaka katangar da aka killace zakunan.

Kanfanin dillancin laran kasar China, Xinhua, ya ruwaito hukumar na cewa, “Daya daga cikin zakunan ya kai wa matashin da ya kutse farmaki a cikin shingen da aka killace su.

“Daga baya aka tabbatar da rasuwarsa a sakamakon raunkan da ya samu, kuma an mika gawarsa zuwa ga dakin ajiyar gawa,” a cewar hukumar.

Ta kara da cewa,  “Muna kara tabbatar wa jama’a cewa babu wani zaki da ya tsere daga gandun dajin,”  kuma ana gudanar da bincike domin gano dalilin abin da matashin ya aikata.

%d bloggers like this: