A ranar Asabar da ta gabata ce mai kula da wani zaki a gidan shakatawa na Hassan Usman Katsina da aka fi sani da Gamji da ke Kaduna mai suna Mustapha Adam ya hadu da fushin zakin da yake kula da shi inda ya damke shi a makogoro, lamarin da ya jawo aka kwantar da shi a asibiti kuma a shekaranjiya Laraba ya ce ga garinku nan.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 12 na rana lokacin da ya je ciyar da zakin a gidan Zoo da ke wajen shakatawar.
Aminiya ta ziyarce marigayin a gadon asibitin kafin ya rasu inda ta tarar da ’yan uwa da abokan arziki sun kewaye shi suna yi masa jaje kan abin da ya faru.
Marigayi Mustapha ya ce “Na kwashe watan takwas ina ciyar da zakin amma a wannan rana sai aka samu kuskure. Domin akwai inda ya kamata a ce na rufe amma sai na manta ban yi haka ba. Lokacin da zakin ya fito kawai sai ya yiwo kaina, sai Sarkin Fawa da ke wajen ne na ji ya yi wa zakin tsawa sai ya fita. Ni dai kawai na ji Sarkin Fawa na cewa Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un da kuma salati shi ne ni ma na dauka ina ta salati.”
Ya kara da cewa: “Sai zakin ya fita sai suka sake kulle wurin sannan aka dauke ni aka ajiye a wani wuri inda ko ya sake fitowa ba zai nufi kaina ba. Daga nan ne aka kawo ni asibitin nan domin duba lafiyata.”
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce zakin ya rike marigayin ne a wuya kuma sai da aka jefa masa nama a cikin kejinsa kafin ya sake shi.”
Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa kusan shekarun zakin uku a wurin shakatawar inda jama’a ke zuwa suna biyan kudi domin kallo.
Sai dai an ce Allah Ya kiyayye a lokacin da zakin ya fito jama’a ba su fara zuwa kallon ba, domin sai bayan azahar ake bude wajen shakatawar.
Matar marigayin, Habiba Yahaya, cikin kuka ta ce, “Gaskiya tunda na samu labarin cewa zaki ya kama shi hankalina bai kwanta ba na kasance cikin damuwa. Yanzu haka muna da ’ya’ya shida da shi kuma a gidan haya muke zaune da shi ,kai abinci ma ba mu da shi. Ko a ranar da abin ya faru cewa ya yi zai je ya nemo ya kawo mana. Muna rokon gwamnati ta taimaka mana da abin da zan kula da ’ya’yansa,” inji ta cikin hawaye.
Sarkin Fawa Sulaiman Sabo shi ne ke samar da nama ga dabbobin kuma Mustapha yaronsa ne wanda kuma yake tare da marigayin a ranar ya ce, “Babu sakaci a cikin lamarin, mutane ne kawai ke fadin abin da ba su sani ba. Zakin nan ba yana bude ba ne ba kuma waje ne da ba a saba shigarsa ba. Amma kaddara ce kawai daga Allah wadda kuma babu makawa sai ta faru. Muna tare muka shiga da nama da sauran abokan aiki. dakin zakin shi ne na farko, zakunan a da su biyu ne amma ambaliyar ruwa ya kashe daya.”
Ya ce, “Kullum Mustapha ne ya fi kowa lura da inda ba a rufe ba, amma a ranar sai Allah Ya mantar da mu. Fitowar Zakin sai na ga abu kamar walkiya, mu dai kawai mun ji kara ne. Ina waigowa sai na ga zakin kife a kan Mustapha. Na ce inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Ina fadi Mustapha na fadi, zakin na jin haka zai ya rabu da shi ya nufi hanyar waje. Ina zuwa kusa da Mustapha sai na ga jini na fitowa daga kunnensa. Ina salati yana salati, daga nan sauran wadanda muke tare da su suka ce in dauko mota domin a kai shi asibiti. Ina fita waje sai zakin ya biyo ni, na yi maza na shige cikin mota. Da na tayar da motar sai ya dakata da na ga haka sai na sake taka motar na yi maza na rufe hanyar komawarsa cikin inda ya fito domin akwai sauran abokan aikina a ciki. Haka muka yi maza muka saka Mustapha cikin mota zuwa asibiti.”
Ya yaba wa ma’aikatan asibitin kan kular da suka ba marigayin wanda bayyana da mutumin kirki mai rikon amana da ya yi matukar bakin cikin rashinsa. Ya ce hukumar gidan zoo din sun yi duk abin da ya kamata wajen nuna damuwarsu da abin da ya faru.