✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yadda za a kawo karshen ci gaba da bazuwar makamai a Najeriya’

“Ya zama wajibi a fito da managartan hanyoyi domin tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinmu."

Wani shehin malami a Sashen Kimiyyar Siyasa kuma shugaban Tsangayar Kimiyyar Dan Adam a Jami’ar Benin da ke jihar Edo, Farfess Augustine Ikelegbe ya ba da shawara kan yadda za a kawo karshen bazuwar makamai a Najeriya.

Shehin malamin yana magana ne yayin wata lakca da aka shirya domin karrama tsohon Daraktan Makarantar Tsara Manufofi da Ba da Horo Kan Shugabanci ta Najeriya (NIPSS) da ke Kuru, marigayi Farfesa Habu Galadima wanda ya rasu a watan Disambar bara.

Farfesan ya kuma ce, “A zamanin da tsoro, fargaba, rashin tabbas, asarar rayuka da dukiyoyi, raba mutane da muhallansu, a bayyane yake a zahiri cewa ‘yan Najeriya yanzu sun fara sabawa da hare-hare a hanyoyi, gonaki, makarantu, gidaje da wuraren neman abincinsu.

“Ana tafka mummunar asarar ta kusan dukkan bangarori na rayuwa wanda hakan yana jawo koma-baya ga ci gabanta.

“Matukar ana so a magance wannan matsalar, dole sai an tsara manufofi wajen dakile yaduwar makamai. Hakan zai hada da yin dokokin da za su karfafa sassan da ke yaki da daukar makaman.

“Ya zama wajibi a fito da managartan hanyoyi domin tsaurara matakan tsaro a kan iyakokinmu, saboda ta nan ne ake shigo da muggan makamai da kuma miyagun kwayoyi da sauran haramtattun kaya.

“A fito da hanyoyin tattarawa da kuma amfani da bayanan sirri wajen magance matsalar. Ya kamata a kara karfafa hukumomin tsaro ta hanyar dibar karin sabbin ma’aikata, ba su horo, karfafa musu guiwa da kuma samar musu da kayan aiki da fasahu na zamani,” inji Farfesan.

Daga nan sai ya ba da shawarar cewa samar da ‘yan sandan jihohi ita ce hanya daya tilo wajen inganta harkar tsaron, yana mai cewa yanzu ‘yan ta’adda sun daina amfani da kananan makamai zuwa manyan bindigogi.

A jawabansu daban-daban, Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya yi magana ta fasahar bidiyo ta Zoom, da Farfesa Sam Egwu, sun bayyana marigayi Galadima a matsayin babban masani, kwararren mai bincike kuma mai sha’awar ganin Najeriya ta ci gaba a zuciyarsa.