✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda yunkurin tsige Shugaban Majalisar Sakkwato ya gaza samun nasara

A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘Yan Majalisar Dokokin Jahar Sakkwato tara suka gabatar da kudirin tsige Kakakin Majalisar bisa zargin barnatar da…

A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘Yan Majalisar Dokokin Jahar Sakkwato tara suka gabatar da kudirin tsige Kakakin Majalisar bisa zargin barnatar da kudi da zama dan amshin shata ga gwamnati, amma lamarin bai samu nasara ba, yayin da bangaren shugaban majalisar suka mamayi takwarorin nasu.

Su na gab da wannan yunkuri ne, sai takwarorin suka fara gabatar da kudirin tsige mataimakin jagoran majalisar, Alhaji Kabiru Ibrahim da Shugaban Majalisar, Alhaji Salihu Maidaji daga karamar Hukumar Gada ya karanta takardar rashin amincewa da aka aiko masa kan mataimakin jagoran.  

“Na karbi takardar neman tsige mataimakin jagoran majalisa daga mutune 21 da suka sanyawa hannu, yin haka na cikin tsarin doka ta 6 ta sashe na 11 karamin sashe 3 dake cikin gyaran fuska da aka yi na 2014 da majalisar dokoki ta yi, don haka sanya hannun ya karbu,” a cewar Maidaji. 

Kalaman shugaban ne suka haifar da hatsaniya da buge-buge har ta kai ga raunuka a hannun dan majalisa daya, Malami Galadanci Bajare, dole ya sanya aka tashi baram-baram kowa ya bar harabar majalisar. 

Honarabul Sani Yakubu dake wakiltar karamar Hukumar Gudu ya zanta da Aminiya kan lamarin “Majalisar Dokokin Sakkwato ba ta taba yin shugaba mai cin hanci kamar Salihu Maidaji ba, kan haka zamu gabatar da dokar tsige shi muna mu 10 muna shirin da mun kai 15 zamu tsige shi, don akwai zarge-zarge na cewa yana tafiyar da kudin majalisa ba bisa ka’ida ba, ya tafi Fakistan ya batar da kudin majalisa miliyan 10 ba da izininta ba, yana amfani da rashin akawun majalisa yana yin yadda ya so a majalisa wajen fitar da kudi, wanda ba zamu sanya ido muna kallonsa ba,” in ji Alhaji Sani. 

Ya kara da cewar “Shugaban ya sanya Sakkwato cikin hadari an samu amincewar karbo bashi na biliyan 100 da gwamnatin Sakkwato ta aiko wa majalisa ba wani abin a zo a gani da za a nunawa talakawan Sakkwato, a halin yanzu dole a samu gyaran jagoranci, Sakkwato ba za ta iya biyan albashi ba nan da wata shekara, dole mu tsaya kan gaskiya da adalci mu kawar da mutane masu rashawa muna tare da karfin gaskiya,” a cewarsa. 

Jagoran Majalisar, Bello Garba Yabo mai wakiltar karamar Hukumar Yabo, ya zanta da wakilinmu bayan ficewarsu a a zauren majalisar, “Abin da ya faru a majalisa ba wani sabon abu ba ne, yana faruwa a wasu wurare, mun yanke shawarar canja mataimaki na ne don ya tafi ya yi taro da wani dan takarar Gwamnan Sakkwato a madadin majalisa, mu ba mu aike shi ba, don haka muna bukatar canja shi, taron siyasa bai dace ba a yanzu ga dokar majalisa,” in ji shi.