✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’ya’ya 2 ga Sarkin Musulumi suka rasu bayan Karamar Sallah

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ya rasa ’ya’ya biyu na ’yan uwansa a rana guda, kwanaki kadan bayan Karamar Sallah.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya rasa ’ya’yan yan uwansa biyu a rana guda bayan Karamar Sallah.

A ranar Asabar, Allah Ya Hussain yi wa S. Adiya da kuma Mu’azu Suleiman rasuwa kimanin kwana uku da Karamar Sallah.

Mu’azu, wanda kani ne ga tsohon ministan wasanni, Yusuf Suleiman, ya rasu ne a yayin da yake cikin koshin lafiya, jim kadan bayan Sallar Subahi.

Shi kuma Hussaini wanda tsohon babban sakatare ne a gwamnatin Jihar Sakkwao, ya rasu ne bayan doguwar jinya.

Dukkanninsu an binne su a makabartar gidan sarautar Sakkwato, wato, Hubbaren Shehu, bayan an yi musu Sallar Jana’iza a Masallacin Sultan Bello da ke garin Sakkwato, wanda Sarkin Musulmi da tsohon ministan da sauran jama’a suka halarta.