✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharram

Ya roki Allah ya kawo wa Nijeriya zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya. ba da umarnin fara duban watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1447 daga gobe Laraba, 29 ga watan Zulhijjan 1446, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yulin 2025.

Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa majalisar Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaid ya raba wa manema labarai.

Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanar wa hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi.

A ƙarshe sanarwar ta ce Sarkin ya roƙi Allah Ya kawo wa Nijeriya zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

Watan Muharram dai shi na wata na farko kalandar Musulunci wanda ake maraba da zuwansa yayin da ake bankwana da shekarar musulunci ta 1446 Bayan Hijira.