✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi

Sarkin ya jadadda muhimmancin girmama shugabanni wajen nemo mafita game da matsalolin talakawa.

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanni yayin da suke bayyana matsalolinsu, inda ya jaddada cewa girmamawa da ladabi sun fi tasiri wajen samun mafita.

“Idan ka zagi shugabanka, ta yaya kake so ya taimaka maka?” in ji shi.

“Amma idan ka yi magana da ladabi, zai saurare ka kuma ya ɗauki mataki.”

Da yake jawabi bayan sallar Idi a Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a da kuma zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

“Ku yi wa Shugaban Ƙasa, Gwamnoni da sauran shugabanni addu’a domin Allah Ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu,” in ji shi.

Ya taya Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan tare da yin kira da su ci gaba da koyi da halaye nagari da suka koya a cikin wata mai alfarma.

Hakazalika, ya jinjina wa malamai kan yadda suka gudanar da wa’azin Ramadan cikin hikima, tare da buƙatar su ci gaba da yaɗa zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma.